Bisa rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah A'arafi, shugaban makarantun addini na ƙasar, ya ziyarci Ayatullah Nouri Hamedani inda suka tattauna, kuma ya gabatar masa da rahoton manyan tsare-tsare da ayyukan da makarantun addinin suke gudanarwa.
A yayin wannan zama, Ayatullah Nouri Hamedani ya yaba da ƙoƙarin Ayatullah A'arafi wajen tafiyar da al'amuran makarantun addini.
Ya nuna jin daɗinsa musamman kan taron karramawa da aka yi wa shahararren malamin nan, Mirzaye Na'ini.
Har ila yau, ya bayyana jawabin da Ayatullah A'arafi ya yi a birnin Najaf (Iraƙi) a matsayin wani babban mataki na nuna darajar ilimi da matsayin fikihu na Ayatullah Mirzaye Na'ini.
Your Comment